Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu da ‘yan uwansu a jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu da ‘yan uwansu a jihar Kaduna

‘Yan bindigar sun kai farmaki kauyen Danhonu da ke garin Millennium a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kai farmaki gidajen ‘yan jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu da matansu da ‘ya’yansu.Wani dangin daya daga cikin wadanda abin ya shafa Taofeeq Olayemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba kafin su aiwatar da aikin na su.


Ya ce sun yi garkuwa da Alhaji Alabelewe da matarsa da ’ya’yansa biyu, yayin da aka yi garkuwa da Alhaji Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya.


Kafin shigarsu gida jen sun farfasa musu kofofinsu da tagoginsu tare da cire duk wani abu da zai hana su shiga gida jen.

Post a Comment

Previous Post Next Post