Sama da gidaje dubu 9,733 suka zube sakamakon guguwar iska a Adamawa – NEMA

Sama da gidaje dubu 9,733 suka zube sakamakon guguwar iska a Adamawa – NEMA

Sama da gidaje 9,733 ne guguwar iska ta shafa a jihar Adamawa a shekarar 2024, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana.

Shugaban sashin ayyuka na musamman a hukumar ta NEMA a Adamawa, Ladan Ayuba ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a Yola.

Ya ce hukumar ta gudanar da tantancewar a kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da, Jada, Hong, Mayo-Belwa, Madagali da Fufore.

Ayuba ya kuma bukaci mazauna yankunan da ambaliyar ta afku da su kaura zuwa wurare mafi aminci ko mafi tsayi domin kare lafiyarsu.

Ya ce gargadin ya zama wajibi ne saboda hasashen Nimet cewa Adamawa na cikin jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwa a shekarar 2024.

Jami’in hukumar ta NEMA ya kuma shawarci mazauna yankin da su rungumi dabi’ar sauraron rediyo don samun bayanai masu dacewa da kuma bin umarnin hukumar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp