Barayin daji sun yi ajalin jami'in Community Watch sun kuma sace shugaban jami'iyyar APC a kauyen Katsina



Wasu 'yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun kai hari kauyen Mai Bakkon Dan Auta da ke mazabar Mai Bakko cikin karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Bayanan da DCL Hausa ta samu daga wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa sun ce barayin dajin sun kashe mutane biyu sun kuma raunata mutane kusan uku.

Kazalika, barayin dajin sun yi awon-gaba da mutane 13, ciki hada shugaban jami'iyyar APC na mazabar Mai Bakko mai suna Alhaji Imamu.

Daga cikin wadanda aka kashe din, kamar yadda DCL Hausa ta samu labari, hada jami'in sa kai na Community Watch daya da ke aiki a yankin.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren Alhamis wayewar Juma'a din nan, inda barayin dajin suka je kauyen kan babura suna harbin kan mai uwa da wabi.

"An yi jana'izar mutanen biyu da aka kashe, wadanda aka ji wa raunuka kuma an garzaya da su asibitin Funtua." In ji majiyar.

Har ya zuwa hada wannan labarin hukumomi ba su ce uffan ba game da batun, bayan da DCL Hausa ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ASP Sadiq Aliyu Abubakar ba ya kusa da wayarsa, bai samu ya dauka ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp