Sabon Fira Ministan Birtaniya Starmer ya yi taron majalisar ministoci na farko

Sabon Fira Ministan Birtaniya Starmer ya yi taron majalisar ministoci na farko

Fira Minista Keir Starmer ya gudanar da taron majalisar ministocinsa na farko bayan samun nasara da yayi a zaben da ya tabbatar dashi a matsayin sabon Fira Ministan Birtaniya


Starmer ya yi maraba da sabbin ministocin, yana mai cewa muna da ayyuka da yawa da za mu yi, don haka yanzu zamu ci gaba da aikinmu.


Daga cikin matsalolin da suke fuskanta sun hada da bunkasa tattalin arzikin kasa mai durkushewa, gyara tsarin kiwon lafiya.


Wani farfesa, a fannin siyasa a Jami'ar Queen Mary ta Landan Tim Bale, ya ce saboda jam'iyyar Labour ta samu gagarumin rinjaye ba ya nufin cewa duk matsalolin da gwamnatin Conservative ta fuskanta sun tafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post