Nijar, Mali da Burkina Faso ba za su koma kungiyar ECOWAS ba - Janar Tiani na Nijar
Shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya bayyana cewa, al'ummar kasarsa, tare da makwabciyarta Mali da Burkina Faso, sun juya wa kungiyar ECOWAS baya.
Ya bayyana hakan ne a yayin bude taro dake gudana a birnin Yamai tsakanin kasashen yankin Sahel uku da suka fice daga babbar kungiyar a farkon wannan shekarar.
Shugaban hukumar ta ECOWAS, Dr Omar Alieu Touray, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya koka da cewa, duk da kokarin da kungiyar kasashen yankin ke yi na dawo da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, amma kasashen uku ba su nuna wata alamar dawowa ba.
A yayin da yake jawabi a wajen bude taro karo na 92 na majalisar ministocin kungiyar a Abuja, ya ce har yanzu kungiyar ECOWAS ba ta kafa tsarin tattaunawa da mahukuntan kasashen Sahel din uku kan matakin da suka dauka na janye mambobinsu daga kungiyar ba.
A ranar 28 ga watan Junairun da ya gabata ne dai mahukuntan kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.