![]() |
Shugaba Tinubu |
A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar a larabar nan,ya ce ma'aikatun da abin ya shafa sun hada da ma'aikatar raya yankin Nije Delta da ma'aikatar wasanni.
Sanarwar ta ce yanzu za a hade ma'aikatun raya yankuna su dawo koma karkashin hukuma daya , kamar hukumar raya yankin Neja Delta, hukumar raya arewa maso yamma, hukumar raya kudu maso yamma, hukumar raya arewa maso gabas.
A cewar sanarwar majalisar zartaswa ta tarayya FEC ta kuma amince da hadewar ma’aikatar yawon bude ido da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki.