Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa jami'an na Hisbah sun kama wanda ake zargin bayan da suka samu korafi daga mijin matar, da ya ce yana zargin akwai kullalliya tsakanin kwamishinan da matarsa.
Bayanai sun ce har yanzu ana tsare da wannan kwamishina a hukumar Hisbah ta Kano.
Mijin matar, ya ce suna da 'ya'ya biyu da su ma ya diga ayar tambaya a kansu.
Hukumar Hisbah ta ce ta kama wanda ake zargin ne da misalin karfe 10 na daren Alhamis tare da matar a lokacin da suke kokarin shiga wani kango mallakin kwamishinan.
Hisbah ta ce a lokacin da aka isa da su hedikwatarta, wanda ake zargin ya amsa cewa ya taba kwanciya da matar sau uku kacal.