Kasar Uruguay ta lallasa Brazil a bugun Fanareti na a gasar cin kofin Nahiyar Amurka

Kasar Uruguay ta lallasa Brazil a bugun Fanareti na a gasar cin kofin Nahiyar Amurka

Uruguay ta fitar da Brazil daga gasar Copa America bayan ta doke ta da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Ba tare da karin lokaci ba a gasar Copa America, wasan ya tashi ne babu ci tsakani, inda aka buga bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan mintuna 90.

Brazil dai ta iya jefa kwallaye biyu ne kawai a bugun Fanareti, yayin da Uruguay ta zura hudu.

Nasarar ita ce ta farko da Uruguay ta samu a kan Brazil a wasanni 13 tun shekarar 2001.

Post a Comment

Previous Post Next Post