Wani Asibiti a jihar Legas ya bayyana cewa suna amsar haihuwar sabbin jarirai 2,500 a kowane wata
Babban daraktan asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH), Farfesa Adetokunbo Fabamwo, ya ce sashin kula da masu juna biyu na asibitin suna ansar haihuwar sabbin Jarirai 2,500 a wata.
Fabamwo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN a Legas.
Yace gidan Ayinke gidane da ake kula da lafiyar mata masu juna biyu da ke cikin harabar asibitin kuma ana yimai lakabi da babban asibitin haihuwa a Nijeriya bayan da aka gyara shi daga maicin gadaje 80 zuwa gadaje 170 da aka samar da na’urorin kiwon lafiya na zamani.
Yace a bangaren ana baiwa mata masu juna biyu ilimin kiwon lafiya a lokacin da ake kula da masu juna biyu sannan kuma ana basu shawarwari kan tsarin iyali da kuma tazarar haihuwa bayan haihuwa a asibitin.