Ku mai dawa ma'aikata kudaden goran sallah da muka basu wanda ku ka karkatar- gwamnan Sokoto

 Ku mai dawa ma'aikata kudaden goran sallah da muka basu wanda ku ka karkatar- gwamnan Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya umurci jami’an hukumar ilimi na kananan hukumomi da da su mayar wa ma’aikatan jihar da aka karkatar kudin alawus din su na sallah Naira 30,000 ko kuma su fuskanci hukunci.


Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da magoya bayansa a gidan gwamnati, da ke sokoto.


Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu jami’an kudi musamman a matakin kananan hukumomi suka hana ma’aikatan su naira 30,000 da gwamnatin jihar ta amince da aba su a matsayin kyautar Sallah.Yace wadanda suka karkatar da wadannan kudade dole ne su dawo da su cikin gaggawa idan ba haka ba za mu dauki tsauraran matakan ladabtarwa a kansu.


Za mu tabbatar da cewa masu laifin sun girbi abin da suka shuka domin ya zama izina ga wasu.


Gwamnan ya tuhumi dukkan shugabannin hukumomin da ake tafka ta’asa da cin hanci da rashawa da su gaggauta tattara duk ma’aikatan da abin ya shafa tare da tabbatar da an mayar wa  da mutanen kudadensu.

Post a Comment

Previous Post Next Post