An kara wa masu sana'ar POS wa'adin kwanaki 60 da su yi rijista da CAC

An kara wa masu sana'ar POS wa'adin kwanaki 60 da su yi rijista da CAC

Hukumar Kula da Kamfanoni da kungiyoyi (CAC) ta kara wa’adin yin rajistar duk masu gudanar da tallace-tallace da karin kwanaki sittin domin daukar wasu da ba su samu damar yin rijistar ba saboda wasu matsaloli na fasaha.


Daily Trust ta ruwaito cewa tun farko hukumar ta bada wa'adin ranar 7 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar da za ta rufe rijistar


A cikin wani sakon da hukumar ta fitar a shafin ta na X, ya bayyana cewa an kara wa'adin da kwanaki sittin wato watanni biyu kenan.


Hukumar Kula da Kamfanoni ta sanar da masu sana'ar (POS) cewa an tsawaita wa’adin farko na 7 ga Yuli, 2024 da aka bayar don yin rajistar na tsawon kwanaki sittin. daga 7 ga Yuli, 2024 zuwa 5 ga Satumba 2024.


Wannan shi ne don ba da isasshen lokaci ga Ma'aikata musamman waɗanda ke cikin lungunan da za su iya fuskantar ƙalubalen hanyar sadarwa don haka su yi rajista kuma su ci gaba da kasuwancinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post