APC ce ke juya akalar PDP a Nijeriya - Mustapha Inuwa

Nyesom Wike da Mustapha Inuwa 

Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma jigo a jam'iyyar PDP a jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, ya zargi jam'iyyar APC da juya akalar jam'iyyar PDP ta hannun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Inuwa ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar, wanda ya gudana Katsina a karshen mako.

Tsohon sakataren gwamnatin wanda ya yi takarar Gwamna a jam'iyyar APC kafin zaben fitar da gwani, ya kuma zargi wasu 'ya'yan jam'iyyar ta PDP a jihar da yi mata zagon-kasa.

Yace "Ba su bukatar jam'iyyar ta yi nasara a dukkanin zabuka, su dai burinsu kawai a ce suna takara, idan za a je taron jam'iyya a Abuja su amso kudin 'daliget', haka kuma idan za a yi zabe sai su amso kudin zabe, idan za a je kotu, sai su amso kudin su sa aljihu".

Mustapha Inuwa ya kara da cewa rikicin da jam'iyyar PDP ke ciki a jihar Katsina ƙirƙira shi aka yi, domin wasu dalilai.

Post a Comment

Previous Post Next Post