An bude taron ECOWAS karo na 65 a Abuja

 An bude taron ECOWAS karo na 65 a Abuja

Gabanin cikar wa'adin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban hukumar ta ECOWAS a ranar 9 ga watan Yulin 2024, a halin yanzu shugabanni da wakilan kasashe mambobin kungiyar suna taro a cibiyar taro na fadar gwamnati dake Abuja. .


An ce taron shi ne babban taron shugabannin kasashen yankin karo na 65,taron na iya sanar da sabon shugaban kungiyar shiyyar Afirka ta yamma da zai jagoranci al'amuransu na tsawon shekara guda.


Sai dai babu wani abin da ya tabbata sai an kammala taron da aka fara da a yau.

Zaman shugaba Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS ya kasance da juyin mulkin da aka yi a wasu kasashe mambobin kungiyar, inda har yanzu ake kokarin dawo da Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso cikin kungiyar kasashen yankin.


Duk kokarin da kungiyar ECOWAS ta yi na dawo da kasashen ya ci tura inda shugaban hukumar Omar Touray ya nuna rashin jin dadinsa a kwanan baya kan kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na kin komawa cikin kungiyar kasashen yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp