Kotu ta umarci Sadiya Farouk ta faɗi yadda aka kashe naira biliyan 729 don raba wa talakawan Najeriya tallafi a 2021

Kotu ta umarci Sadiya Farouk ta faɗi yadda aka kashe naira biliyan 729 don raba wa talakawan Najeriya tallafi a 2021

Babbar kotun tarayyar da ke Legas ta umarci tsohuwar minsitar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan ƙasar na tsawon wata shida.


Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da aka raba akowace jiha.


Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta gurfanar da Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta ‘yancin samun bayanan.


Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma’a.


Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowane ɗan ƙasa ciki har da SERAP.


Don haka kotu ta umarci tsohuwar ministar ta yi bayanin yadda ta kashe naira biliyan 729 wajen raba wa talakawan Nijeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021, kamar yadda hukuncin ya nuna.


Mai shari’a Dipeolu, ya kuma ce dole ne tsohuwar ministar ta yi wa SERAP cikakkun bayanan hanyoyin da aka bi wajen zaɓo mutanen da suka amfana da tallafin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp