Jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Katsina na nuna wa juna yatsa

Sanata Lado da Dr Mustapha


Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP a jihar Katsina sai ƙara tsami yake bayan da jam'iyyar ake ganin kamar ta ta rabu gida biyu.

Yanzu haka dai tsakanin PDP tsagin tsohon dan takarar Gwamna a shekarar 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke da kuma tsagin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr Mustapha Muhammad Inuwa ya ja tunga.

Jam'iyyar PDP tsagin Sanata Yakubu Lado DanMarke ta zargi dan majalisar wakilan Nijeriya mai wakiltar kananan hukumomin Mashi/Dutsi Hon. Salisu Yusuf Majigiri da yi wa jam'iyyar APC aiki alhalin yana cikin jam'iyyar PDP don hanata kaiwa ga nasara a zaben 2023 da ya gabata.

A taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar jam'iyyar PDP da ke Katsina, kakakin jam'iyyar Lawal Audi Yar'adua, ya ce akwai hujjoji masu kwari da suka nuna yadda Hon Majigiri ya rika yi wa jam'iyyar ta PDP ribar albarka kafin da kuma lokacin zaben da ya gabata duk don zagon-kasa da hakan ke nuna karara yadda ya yi wa APC aiki.

"Idan aka yanka jikinka, jinin Shema ne za'a gani domin APC ke jikinka, muna da bayanai wadanda ke nuna cewa alakarku tana nan bata lalaceba, in ji shi.

"Kuna yi wa jam'iyyar PDP zagon kasa ne, kuna ƙoƙarin hama jam'iyyar PDP ta yi wani tasiri cikin harkokin ta, mun san APC kake ma aiki". A kalaman Lawal Audi Yar'adua.

Jam'iyyar ta kuma zargi Majigiri da Salisu Uli da Sanata Tsauri da sauran wasu jiga-jigai a bangaren su na kokarin lalata jam'iyyar PDP a jihar Katsina 

Wannan zargi dai na zuwa ne bayan sa'o'i kaɗan da tsagin jam'iyyar na ɓangaren Dr. Mustapha Muhammad Inuwa suka gudanar da 
taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a jihar, inda suke nuna yatsa ga PDP bangaren Sanata Yakubu Lado DanMarke.

A taron manema labarai da PDP tsagin Mustapha Inuwa ya gudanar a karshen mako ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ce ke juya akalar jam'iyyar PDP a Nijeriya ta hannun ministan Abuja Nyesom Wike.

Post a Comment

Previous Post Next Post