Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta sanar da haramta duk wani nau'in caca da harkar mata masu zaman kansu wato sana'ar karuwanci a duk fadin jihar.
Bayanin hakan na cikin wani kunshin dokoki da hukumar ta fitar a Katsina daga ofishin babban Kwamandan hukumar Dr Aminu Usman Abu Ammar, inda ta ce ta kuma haramta masu sana'ar haya da babura wato "achaba" su rika daukar mata sama da daya ko goyon mace da namiji a kan baburansu.
Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne bisa la'akari da lalacewar tarbiyya da ke neman ya yawaita a cikin al'umma.
Hukumar ta ja hankalin iyaye da su saka idanu sosai kan 'ya'yansu, domin tarbiyya ta inganta a cikin al'umma.
Kunshin dokar ya kuma sanar da haramta wa 'yan acabar saka gajeren wando da askin banza a yayin gudanar da sana'arsu.
Kazalika, hukumar ta kuma sanar da haramcin sanya labule ga masu tuka Keke-Napep, da haramta daukar mace a gaban Keke-Napep din. Sannan hukumar ta hana a sanya maza da mata a cikin Keke-Napep guda.
Kunshin dokar ya kuma haramta wa masu tuka Keke-Napep saka gajeren wando tare da saka kayan kida da kure sauti a babur din mai kafa uku.
Sannan kunshin dokar ya kuma hana masu tallar maganin gargajiya su yi amfani duk wani nau'i na kalaman batsa a yayin tallolinsu da kuma umurtarsu su kashe lasifika a duk lokacin da za a yi sallah a masallatai.
Hukumar ta ja hankalin cewa duk wanda ya karya wadannan dokoki akwai hukunci mai kwari da ta tanada.