Kura ta kufce daga hannun jami'an gwamnati a Jos

 


Hukumar kula da yawan shakatawa ta jihar Filato da ke Nijeriya ta sanar da kufcewar wata kura daga gandun daji mallakin jihar da ke a Jos. 

A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce ta baza jami'anta domin nemo dabbar a sassan jihar, inda ta ce za ta yi amfani da jirgi mai sarrafa kansa a kokarin gano kurar.


Hukumar ta shawarci mutane da ka da su yi wa kurar komai, a duk inda suka ganta su sanar da jami'anta ta lambar waya 09026927620 ko kuma 09131000945

Post a Comment

Previous Post Next Post