Dan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana damuwarsa kan tsadar rayuwa da karancin abinci da kasarnan ke fuskanta.
Hakan na a cikin wata hira da BBC Hausa tayi da Sanata Ndume, ya ce gazawar gwamnatin tarayya na magance wadannan matsaloli babban kalubale ne, inda ya kara da cewa wasu ministoci sun kasa ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan lamarin.
Sanatan ya kara da cewa hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar ‘yan Najeriya miliyan 82 za su fuskanci karancin abinci nan da shekaru biyar masu zuwa.
Ndume ya yi magana ne jim kadan bayan da abokin aikinsa Sanata Sunday Steve Karimi, ya gabatar da kudirin neman magance matsalar karancin abinci a kasar.
Sanatan ya ce makasudin gabatar da kudirin shi ne jawo hankalin gwamnati kan tsananin karancin abinci da ke addabar ‘yan Najeriya da dama.