Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar abinciMajalisar dattawan Nijeriya ta tabka zazzafar muhawara a ranar Talata, inda tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar yunwa da ake fama da ita a kasar.

Majalisar ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki matakan yaki da matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar ta hanyar zayyana wasu matakan yaki da lamarin.

Majalisar dattijai ta yi nuni da cewa, a cikin ‘yan watannin da suka gabata an samu hauhawar farashin kayan masarufi a kasar nan, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Post a Comment

Previous Post Next Post