Filayen jiragen sama uku ne daga cikin 22 ke samun riba a Nijeriya - FAAN


Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN, ta ce filayen tashi uku ne kawai daga cikin filayen jiragen sama 22 da Nijeriya ke samun riba.

Manajan Daraktan FAAN, Olubunmi Kuku ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Ta yi nuni da cewa, ana bayar da tallafin filayen jiragen sama 19 ne saboda ba sa samun zirga-zirgar fasinja daidai da kudin da ake kashewa.

A cewarta, akasarin filayen tashi da saukar jiragen sama 22 da FAAN ke kula da su na bukatar a inganta muhimman ababen more rayuwa a cikin su.

Post a Comment

Previous Post Next Post