Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tinubu tayi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tinubu tayi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA

Bayan wani kudiri na gaggawa wanda mambobin majalisar wakilai 88, suka suka gabatar, majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar ta Samoa har sai an gama bincike.


Da yake gabatar da kudirin a ranar Talatar nan, dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Dala a kano, Aliyu Madaki, ya ja hankali kan batun da ke nuna “daidaitan jinsi” tare da duk wasu batutuwa dake dake haifar da cece kuce.


Majalisar ta kuma umarci kwamitocin dake da alaka da yarjejeniya ta kasa da kasa da su binciki kudurorin yarjejeniyar da ke cike da ake ta cece-kuce akai.


Takaddama dai ta kunno kai kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta rattaba hannu da kungiyar Tarayyar Turai, inda da dama suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin Nijeriya ta amince da yarjejeniyar.


Yarjejeniyar ta Samoa ta haifar da cece-kuce a yanar gizo tare da wasu da dama da ke adawa da yancin LGBT, wanda ya sabawa dokar hana auren jinsi da ma'auratan da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa a shekarar 2014.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp