Rundunar sojojin Nijar ta hallaka 'yan ta'adda sama da 100 a sabon farmaki

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1wxxPQ8U769PsvIhqS5Hj3jv-T7F1CLG7

A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan rana ta Alhamis, rundunar sojojin Nijar din ta sanar da samun nasarar kashe 'yan ta'adda sama da 100 a yayin wani farmakin ramuwar gayya da ta kai  ta sama da kasa a kan wadanda take zargi da kisan sojojin kasar 20 a yankin Tassia da ke cikin karamar hukumar Téra na jihar Tillaberi a ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata

Kazalika sanarwar rundunar tsaron kasar ta ce daga ranar daya zuwa uku ga watan nan wani samame da ta kai a cikin kasuwannin Dougouro da Bankilare dukkan su cikin karamar hukumar ta Téra ya bata damar hallaka 'yan ta'adda 8 da kuma kama wasu 19 

A dabra guda kuma rundunar ta ce a ranar daya ga watan dai na Yulin nan da muke ciki ta yi nasarar kashe wasu 'yan ta'addar 20 tare da ragargaza kayan aikinsu a yayin wani barin wuta da ta musu a maboyarsu ta sama da ke da nisan kusan kilomita 4 daga arewa da Kokoloko da ke kan iyaka da Burkina Faso

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp