Kotu ta saka ranar da Ganduje zai san makomarsa a shugabancin APC


Kotun tarayya a Abuja ta saka 18 ga watan Satumbar, 2024 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan taƙaddamar shugabancin jam'iyyar APC ta kasa da Abdullahi Ganduje ke jagoranta.

Hon Abdullahi Saleh Zazzaga, jagoran kungiyoyin jam'iyyar APC na yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya ne dai ya jagoranci mutanensa, suka garzaya kotu neman sai Abdullahi Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC.

'Yan yankin Arewa ta tsakiyar dai na cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar ne ya ba su damar a ba su shugabancin jam'iyyar tun da wanda ya sauka daga bangarensu yake, kuma ba wa'adin mulkinsa a kare ba.

Alkalin kotun tarayyar Mai Shari'a Inyang Ekwo ya saka 18 ga watan Satumba na wannan shekarar domin yanke hukunci a kan wannan sa-toka-sa-katsi.

Post a Comment

Previous Post Next Post