Ita kuwa kasuwar Mai'adua jihar Katsina farashin dai bai gusa ba daga na makonni biyu da suka gabata da aka saya N95,000.
Sai dai a kasuwar Karamar Hukumar Gombi a jihar Adamawa masarar ta sauka a jiya, inda aka sayar da buhun masarar N90-95000, bayan da a makon jiya aka sayar N100-102,000
An samu sauƙin N7000 a mako guda.
N90,000 cif aka sayi buhun masara a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan, bayan da a makon jiya aka saya N88,000.
A kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi buhun masara mai cin tiya 40 N87,000-90,000 a satin nan, amma a makon da ya wuce N85,000-88,000 aka sayar da buhun masara a kasuwar.
Sai kuma kasuwar Dawanau jihar Kano,an sayi buhun masara N87,000 a makon farko na watan Yulin shekarar 2024, yayin da makon jiya aka sayar N85,000 nan ma an samu ragin 2000 cif.
Ita kuwa Shinkafar Hausa na ci gaba da sauka a kasuwar Mai'adua jihar Katsina wanda ake sayar da buhunta N140,000 a wannan satin, amma a satin da ya kare N145,000 ake sayar da buhun shinkafa 'yar gida.
Sai dai farashin shinkafar ya bambanta da na kasuwar Dandume a jihar Katsinan, inda aka sayar da buhun N157-160,000 a makon nan, amma a makon da ya gabata N140-170,000 ake sayar da buhun,ya dai danganta da kyan Shinkafar.
A kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi buhunta N150,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka saya N155,000, an samu sauƙin 5000 kenan a wannan mako.
Shinkafar dai na ci gaba da sauka a sassan kasuwannin kasar nan, N150,000 cif aka sayar da buhun shinkafar Hausa a kasuwar Dawanau da ke jihar a wannan mako, bayan da a makon jiya aka saya N155,000.
Sai dai a jihohin Adamawa da Legos N160,000 aka sayar da buhun shinkafar a makon nan, bayan da a makon da ya gabata aka saya N150,000 a Karamar Hukumar Girie a jihar Adamawa.
Shinkafar Bature kuwa ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da aka saya N90,000 daidai a satin nan, yayin da a satin da ya shuɗe aka sayar N87,000.
To a kasuwar Giwa jihar Kaduna N88,000 aka sayi buhun Shinkafar Bature a wannan satin, farashin dai bai sauya da na makon jiya.
N82,000 ake sai da buhun shinkafar waje a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan makon, inda a makon jiya aka sai da N81,500.
A jihar Legas da ke kudancin Najeriya N80,000 ake sai da Buhunta a makon nan,haka farashin yake a makon jiya.
Sai kuma kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa aka N78,000 a satin nan da ke dab da ƙarewa, amma a makon da ya gabata N67,500 kuɗin buhun Shinkafar waje yake a kasuwar.
Ga ma'abota cin alala da kosai sai in ce ku gyara zama don jin yadda farashin wake yake a wasu daga cikin kasuwannin kasar.
Farashin farin wake dai bai sauya tufafi ba da na makon jiya da aka saya N250,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas.
Haka zalika farashin waken bai canza daga na makon da ya gabata da aka sai da N165-170,000 a kasuwar Gombi a jihar Adamawa.
Sai kasuwar Dandume jihar Katsina aka saya N190-194,000 a satin nan, yayin da a makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi N180-190,000 a kasuwar.
Ita kuwa Kasuwar Giwa jihar Kaduna N180,000 ake sayar da Buhunta a wannan makon, amma a makon Jiya N175,000 kuɗin buhun fari wake.
A Kasuwar Dawanau jihar Kano N170,000 ake sayar da buhun farin wake a wannan makon, yayin da a makon da ya shude aka N178,000, an samu canjin N8000 kenan a mako guda.
N175-180,000 ake sai da buhun wake a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, amma a makon jiya N175,000 ake sayar da buhunta.
Kwalin taliya ma ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar da ake saidawa N18,000 a satin nan, inda a satin da ya gabata aka saida kan kudi N17,000 .
A kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi kwalinta N16,000 cif a makon nan, yayin da a makon jiya aka saya N13,700. Karin N2300 kenan a mako ɗaya .
Sai kuma kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa farashin kwalin taliya ya tashi a makon nan,wanda aka saya N16,000,sai dai a makon daya gabata N13,000. Ake sayar wannan ma an samu karin N3000 a sati guda.
A Mai'adua jihar Katsina da kasuwar Dandume a jihar N15,500 ake sayar da kwalin taliyar a makon nan.
To bari mu karkare farashin kayan abinci na makon nan da farashin kwalin taliya a kasuwar Giwa jihar Kaduna,an sayi kwalinta N15,000 daidai a makon nan, yayin da a makon jiya aka sayar N14,000 cif.
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a watan Mayun shekarar 2024, ya nuna cewa farashin kayakin abinci ya haura da kashi 33.90%.
DCL Hausa A'isha Usman Gebi