Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin tsare wata babbar jami’ar Sibil difens mai suna Mrs Tosin Olagunju, a gidan yari na Suleja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito, mai shari’a Binta Nyako ta bayar da wannan umarni ne bayan an gurfanar da Olagunju a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da damfarar masu neman aiki da sauransu.
An zargi Mrs Tosin Olagunju da karbar Naira miliyan 12.4 daga hannun masu neman aiki, tare da alkawarin cewa tana da karfin da za ta ba su aikin na Sibil Difens.