Majalisar dokokin jihar Kano ta karyata rade-radin da ake yadawa kan batun zaman majalisar, lamarin da aka jingina da rashin tsaro, wanda ya samo asali daga rikicin masarautar jihar.
Kakakin Shugaban Majalisar, Kamaluddeen Shawai ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Laraba.
Yace labarin da ake yadawa ba gaskiya bane "karya ne kuma maras tushe".
Shawai ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da duk wani rahoton da ke nuni da cewa majalisar ba ta sake bude zauren majalisar saboda rashin tsaro da rikicin masarautar ya haifar.
"Majalisar za ta dawo zamanta nan ba da jimawa ba," in ji shi.