Kimanin mutane 63 ne ake zargin sun rasa rayukansu yayin da 2,102 ake zargin sun kamu da cutar ta kwalara a fadin jihohi 33 tun daga farkon wannan shekarar.
Darakta Janar na hukumar da ke yaki da cututtuka a Najeriya, Dakta Jide Idris ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake karin haske kan bullar annobar.
Ya ce jihohi 10 da suka fi yawan masu cutar sun hada da Legas, Bayelsa, Abia, Zamfara, Bauchi, Katsina, Cross River, Ebonyi, Ribas da Delta.