Kudaina muzgunawa ma'aikatanmu yayin da suke kan aiki- FRSC

Kudaina muzgunawa ma'aikatanmu yayin da suke kan aiki- FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa da su daina muzgunawa jami’anta a yayin gudanar da ayyukansu a fadin kasar nan.


Shugaban hukumar FRSC, Malam Shehu Mohammed ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake mayar da martani kan hukuncin da wata kotun majistare ta yanke na daurin shekaru uku a gidan yari bisa laifin cin zarafin jami'an hukumar.Shugaban ya nuna jin dadinsa da hukuncin da aka yanke tare da jinjina wa bangaren shari’a kan yadda ake gudanar da adalci cikin gaggawa.


Ya kuma nanata kudurin rundunar na hada kai da bangaren shari’a wajen gaggauta hukunta masu laifi musamman wadanda ke cin zarafin jami’an ta a kan hanyoyi da ke fadin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post