Jirgin farko na alhazan jihar Kano 554 zai taso zuwa gida Nijeriya

 Jirgin farko na alhazan jihar Kano 554 zai taso zuwa gida Nijeriya

Kimanin alhazan jihar Kano kimanin dari biyar da hamsin da hudu (554) sun kammala shirye-shiryen komawa gida a jirgin farko.


Babban Daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana haka a yau a yayin ban kwana da mahajjata a Unguwar Kudai da ke birnin Makka na kasar Saudiyya.


Wannan ya biyo bayan jadawalin da hukumar jin dadin alhazan da Max Air suka tsara, kamar yadda aka gani a makon da ya gabata. Lamin Rabi’u ya bayyana cewa wadanda suka zo na farko su ne za su fara komawa gida.


Kananan hukumomin da aka tantance sun hada da Gwale, Dala, Ungogo, da Fagge. Ya bukaci daukacin alhazai da su ci gaba da zaman lafiya da hakuri. Yace dukkanin mahajjata za su ci gaba da samun abinci, magunguna, da duk wata kulawar da ta dace har zuwa har zuwa lokacin da zasu dawo.


Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa wanda daraktan ayyukan hajji Alhaji Kabiru Muhd Panda ya wakilta ya yi kira ga wadanda suka dawo da su kula da kyawawan dabi’u kamar yadda suke yi a da da kuma ci gaba da addu’ar samun nasara a wannan aikin.


Jirgin zai taso ne daga filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz a Jidda a yau zuwa filin jirgin Malam Aminu Kano tare da alhazan jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp