Kada ku bari tsaro ya sake tabarbarewa a yankin arewa maso Gabas - Atiku Abubakar

Kada ku bari tsaro ya sake tabarbarewa a yankin arewa maso Gabas - Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai a jihar Borno, yana mai rokon gwamnatin tarayya da kada ta bari tsaro ya sake tabarbarewa a yankin arewa maso Gabashin kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook , inda ya zargi gwamnatin da rashin kishi wajen tsayawa tsayin-daka kan nasarorin da jami’an tsaro suka samu wajen yakar ayyukan ta'addanci a yankin.

Atiku Abubakar ya ce abin bakin ciki ne cewa abubuwa irin wadannan na cigaba da faruwa a yankin Arewa maso Gabas don haka dole a tashi tsaye domin kawo karshensu.

Ya ce ya kamata gwamnantin tarayya ta tashi tsaye wajen yakar irin wadannan tashe-tashen hankula domin ganin cewa ba a sake samun faruwar hakan a nan gaba ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post