Kungiyar NASAN ta roki Sanata Wamakko ya sa baki kan yunkurin taba rawanin Sarkin Musulmi a Sokoto

Kungiyar wayar da kai ta tsatson Sullubawa mai suna National Association of Sullubawa Awareness of Nigeria ta rubuta wasika ga Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu kan batun Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Wasikar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Comr Usman Muhammad Garba ta yi kira ga Gwamnan jihar da ya janye duk wani yunkuri na taba fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi da sunan rage mata karfin ikon da take da shi a halin yanzu.

A cikin zungureriyar wasikar, Comr Usman Muhammad Garba ya bayyana cewa Mai alfarma Sarkin musulmi shugaba ne da ke da martaba da kuma gadajjiyar daraja ta Mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodio.

Comr Usman Muhammad Garba duk a cikin wasikar ya yi kira ga uban wannan kungiya Sanata Aliyu Magatakarda Wamako da ya saka baki cikin wannan al'amari don samun maslaha. 

Wasikar ta kare da addu'ar Allah ya taimaki majalisar Sarkin Musulmi, gwamnatin jihar Sokoto da tarayyar Nijeriya baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp