Kada ku maimaita irin abinda Buhari ya yi a. mulkinsa - Kiran Shehu Sani ga Tinubu

Kada ku maimaita irin abinda Buhari ya yi a. mulkinsa - Kiran Shehu Sani ga Tinubu
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya sake maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a fannin nada mukamai.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake hira ta cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels yayin da ya zargi Buhari da son zuciya a lokacin da yake kan mulki musamman wajen nada mukamai.

Ya shawarci shugaba Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan kada ya tafka kura-kurai irin na shugaba Buhari, yace akwai ministoci da dama da ake gani akwai matsala a ayyukansu amma saboda 'yan lele ne aka ki tabuka komai a kansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post