Jirgin sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a Kaduna

Jirgin sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a Kaduna


Wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) ya yi hatsari a safiyar ranar Litinin a kauyen Tami da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na asuba, bayan da suka ji kara mai karfi daga wurin da hatsarin ya auku, inda suka bayyana cewa matukin jirgin ya fito daga cikin tarkacen jirgin.

Wani ganau ya ce tawagar jami’an soji daga rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin tabbatar da tsaron yankin tare da gudanar da bincike na farko

Sun killace wurin da hadarin ya afku domin hana shiga ba tare da izini ba da kuma tabbatar da tsaron mutanen kauyen. Jami’an sun kuma fara tantancewa ta farko don gano musabbabin hadarin, wanda har yanzu ba a tabbatar da dalilin faruwar sa ba.

Har ya zuwa lokacin jaridar The Nation ta hada wannan rahoto, rundunar sojin saman Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba, amma ana sa ran za a gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin jirgin.

Post a Comment

Previous Post Next Post