Mazauna Kaduna, Kano da Katsina na fama da tashin farashin abinci a kasuwanni

Mazauna Kaduna, Kano da Katsina na fama da tashin farashin abinci a kasuwanni


Al'ummar Nijeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin abinci da ba a taba yin irinsa ba.


Binciken da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya fitar ya nuna cewa a jihohin Kaduna, Kano da Katsina, al'ummar jihohin na fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci.


A wani bincike da NAN ya gudanar a jihohin ya nuna cewa ana samun karuwar farashin shinkafa, biredi, sikari, garri, nama da kwai da dai sauran su, wadanda su ne abubuwan da ake amfani da su a gidaje.


Hauhawar farashin ya yi tasirin gaske ga al'umomin da suke jihohin, wanda hakan ya sa wasu gidajen ba su iya cin abinci sau uku a rana kamar yadda aka saba.


Binciken ya gano cewa mazauna Kaduna,Katsina da kuma Kano na kokawa bisa yadda kayan abinci suke tashin gauron zabi inda suka bayyana cewa kullum kayan kara tashi suke yi ba tare da wani dalili ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post