Jihar Kaduna ta kammala jigilar kwaso Alhazanta daga kasa mai tsarki


Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta ce ta kammala jigilar dawowa da alhazanta sama da 4000 daga kasar Saudiyya zuwa Nijeriya.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Mohammed Abdullahi, ya ce jirgin karshe na dauke da mutane 56 a jirgin Max Air, wanda galibin su jami'an hukumar ne.

Kakakin ya kara da cewa jihar Kaduna ce ta fi yawan alhazai wanda yakai 4,767, duk kuwa da asarar rayuka da aka yi a kasa mai tsarki.

Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar Malam Salihu .S. Abubakar ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa jajircewarsa kan 


Post a Comment

Previous Post Next Post