Jami'ar FUDMA ta zargi wani ma'aikacinta da kwarmata wa 'yan bindiga bayanan sirrin jami'ar

Jami'ar FUDMA ta zargi wani ma'aikacinta da kwarmata wa 'yan bindiga bayanan sirrin jami'ar

Shugaban jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) ta Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya yi zargin cewa wasu ma’aikatan jami’ar suna bai wa barayin daji bayanai ne.


Bichi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina a ranar Talata, ya ce ma’aikatan da ake zargin an baiwa wata hukumar tsaro domin ci gaba da bincike akai.


Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar da ake zargin sun kai hari a yankin, inda suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan jami’ar da kuma ‘yan uwansu.Wani harin da aka kai kwanan nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin ma’aikatan jami’ar ya sa abokan aikinsa gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin tsaro da yake karuwa.


A cewar shugaban jami'ar, hukumar gudanarwar makarantar na yin duk mai yiwuwa don hana afkuwar irin wannan lamari amma lamarin sai kara ta’azzara yake yi.


Bichi ya ce, Wannan batu na masu ba da bayanai ga 'yan bindiga abin damuwa ne, don haka, mun binciki wadanda muke zargi da bayar da bayanan abokan aikinsu da daliban.


Mun same su kuma mun mika ga daya daga cikin jami’an tsaro domin ci gaba da bincike akai

Post a Comment

Previous Post Next Post