Firgici ya kunno kai a Rano da ke Kano bayan da wasu masu kama da ‘yan daba suka mamaye fadar masarauta

Firgici ya kunno kai a Rano da ke Kano bayan da wasu masu kama da ‘yan daba suka mamaye fadar masarauta

A cikin wata wasika da aka rubuta wa kwamishinan ‘yan sandan jihar, jaridar SolaceBase ta rawaito cewa ‘yan dabar sun yi sansani a fadar Sarkin Rano tun a ranar Lahadi da wasu da ba a tantance ko suwaye ba.


Ta ce har yanzu ba a san dalilan wadannan mutane masu dauke makamai ba, ana daukar zaman nasu a matsayin barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyi al'ummar yankin.


A cewar wasikar, mazauna masarautar Rano mutane ne masu zaman lafiya da kullum suna gudanar da harkokinsu ba tare da haifar da tarzoma ba.


Ta ce a tsawon shekaru masarautar Rano ta samu zaman lafiya ba tare da wata matsala ba kuma hukumomin tsaro na iya shaida wannan tarihin da masarautar ke da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp