An saka lokacin sake kidayar yawan al'ummar Nijeriya

An saka lokacin sake kidayar yawan al'ummar Nijeriya

Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta ce zatayi kidayar 'yan kasar a watan Nuwamba, 2024, don kidayar yawan al'umma da gidaje a Nijeriya.


Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai na bikin ranar yawan jama’a ta duniya na shekarar 2024, shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra, ya ce shawarar hakan ta kasance bisa amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu.


Kwarra, wanda ya bayyana cewa hukumar ta shirya kashi 70 cikin 100 na gudanar da kidayar, ya ce jinkirin da Nijeriya ke samu na samun bayanan al’ummarta ba zai hana kasar samun nasarar kidayar yawan jama’a da gidajen dake kasar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post