INEC ta gabatar da shawarwari 142 don inganta harkokin zabe a Nijeriya

INEC ta gabatar da shawarwari 142 don inganta harkokin zabe a NijeriyaShugaban hukumar zabe ta mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu,ya ce hukumar tana shirin gabatar da shawarwari 142 domin inganta harkokin zabe a nan gaba.

Yakubu ya bayyana haka ne a wajen bude taron karramawa na kwanaki biyu ga kwamishinonin zabe,a ranar Litinin a Legas.

Ya ce hukumar ta wallafa rahoton sake duba zaben shekarar 2023, inda ya ce tuni aka samu a shafinta na intanet.


Zan iya gaya muku cewa hukumar zabe ta bayar da shawarwari 142 kan inganta harkokin zabe a Nijeriya da ake shirin gabatar dasu.

Da zaran an shirya rahoton, za mu fito fili mu tattauna da ‘yan Nijeriya kan wannan batu domin yana da muhimmancin gaske garesu.

Sauye-sauyen akasari ana aiwatar da su ne ta hanyar gudanar da aikin hukumar ta INEC, amma wasu jami’an tsaro ne za su aiwatar da su a lokacin zabe da zarar an tabbatar dasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post