Mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayinda da 53 suka jikkata a wani hadarin mota a Kano

Mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayinda da 53 suka jikkata a wani hadarin mota a Kano

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa reshen jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar matafiya 25, yayin da wasu 53 suka samu raunuka a wani hatsarin mota.


Hatsarin ya afku ne da sanyin safiyar Litinin a kusa da Kasuwar Dangwaro, dake hanyar zariya a Kano.


Matafiyan sun yi lodi ne a cikin wata tirela wadda take dauke da shanu ta da zata tafi yankin kudancin Nijeriya daga Maiduguri.

A cewar kwamandan hukumar FRSC a jihar, Ibrahim Abdullahi, hatsarin ya afku ne da wata tirela (IVECO) mai lamba XA 311 ZB.


Yace an kira su ne da misalin karfe 03:15 na daren ranar 1 ga Yuli, 2024. Da samun labarin, suka yi gaggawar aika jami’ai da motar  zuwa inda lamarin ya faru domin ceto wadanda lamarin ya shafa da karfe 03:30.


Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon gudun wuce gona da iri da motocin keyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post