'Yan bindiga sun sace mutane 7 a Maradi Jamhuriyar Nijar
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutune bakwai a gidaje hudu daban-daban a wani kauye mai suna Badariya da ke da nisan kilomita 5 da karamar hukumar Gabi ta jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Cikin wadanda aka sacen cikin dare sun hada da mata biyu, yara kanana biyu da kuma magidanta guda uku.
Kazalika wasu maharan na daban sun yi awon-gaba da wasu 'yan mata biyu da shanu biyu a kauyen Gidan Dan Komo da ke cikin karamar hukumar dai ta Gabi a jihar Maradi.