Gwamnatin Nijeriya za ta dakatar da kwangilar aikin hanyar Lokoja da Benin

Gwamnatin Nijeriya za ta dakatar da kwangilar aikin hanyar Lokoja da Benin 

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin dakatar da ayyukan da ‘yan kwangilar ke gudanarwa na gyaran hanyar Lokoja zuwa Benin saboda jinkirin aikin da rashin nuna damuwa da halin da al'ummar yankin ke ciki ga 'yan kwangilar dake aikin.


Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Uyo,inda ya koka da yadda aikin gyaran hanyar baya sauri.


Ministan kuma ya yi gargadin cewa duk dan kwangilar da ya ci gaba da jan kafa game da aikin da gwamnati ta bashi za'a soke kwangilar sa.


Haka kuma akwai shawarwarin da gwamnatin tarayya ta yi na tallafa wa ‘yan kwangilar dake cikin gida Nijeriya, wanda zai yi  tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin masu aikin gaba daya

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp