Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitoci biyu da zasu yi yaki da ciwon zazzabin cizon sauro

Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitoci biyu da zasu yi yaki da ciwon zazzabin cizon sauro

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bada shawara kan kawar da zazzabin cizon sauro a Nijeriya (AMEN) da kuma kwamitin ministoci na yaki da zazzabin cizon sauro a yunkurinta na kara kaimi wajen kawar da cutar zazzabin cizon sauro.


Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate a lokacin da yake kaddamar da kwamitin ba da shawara da kwamitin ministocin, ya ce matakin ya zama wajibi bisa la’akari da gagarumar matsalar da cutar ke da shi a Nijeriya ta fuskar mace-mace, yada wasu cutukan tsakanin al'umma.


A cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da kasashen waje Tashikalmah Hallah, ministan ya jaddada cewa, duk da cewa ana iya yin rigakafi da kuma magance cutar,amma zazzabin cizon sauro na ci gaba da zama babban kalubale ga kasar.


Don haka, akwai bukatar cigaba da nemo hanyoyi tare da shawarwarin masana da zasu taimaka wajen kawo karshen sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp