Nijeriya na bukatar tsarin shugabanci irin na su,Tafawa Balewa,Sardauna da Nmandi Azikiwe

Nijeriya na bukatar tsarin shugabanci irin na su,Tafawa Balewa,Sardauna da Nmandi Azikiwe

An bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba tsarin da Abubakar Tafawa Balewa da Dr Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo da Sir Ahmadu Bello da sauran magabata suka yi domin shawo kan kalubalen tattalin arziki da siyasa da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.


Babban kodinetan kungiyar National Unity Pathfinders (NUP) na kasa Ambasada Sixtus Obinna Nwoke da sakataren kasa Saleh Alhassan Kubah injiniya ne suka yi wannan kiran a Abuja a wajen taron kaddamar da kwamitin gudanarwa na kungiyar (CWC) na kungiyar.


Sun ce kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu ba za a iya tsallakewa ba, kuma sake duba tsare-tsare da abubuwan da suka gada na shugabannin kasar da suka kafa kasar zai taimaka wajen samar da mafita kan kalubalen.Saboda irin namijin kokarin da tsoffin shugabannin da suka yi kokari wajen ganin an samu hadin kai da ci gaban Nijeriya."A yau, mun taru a matsayin masu neman hanya don tsara sabuwar hanya ga ƙasarmu domin samun mafita ga halin da kasar ke ciki


Mun hada kai wajen neman kasar Nijeriya da ta dace da muradun kasar da muke so, muna hasashen Nijeriya za ta kasance da hadin kai, sanin yanci da kuma sadaukarwar ‘yan kasar baki daya domin shawo kan duk wata matsala da ta addabi kasar baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post