Hukumar kwastam ta kama bindigu 844 da alburusai 112,500 aka shigo dasu Nijeriya

Hukumar kwastam ta kama bindigu 844 da alburusai 112,500 aka shigo dasu Nijeriya

Babban Kwanturolan Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya (NCS) Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana yadda aka kama bindigogi guda 844, alburusai 112,500 da sauran haramtattun kayayyaki da aka kama a tashar jirgin ruwa ta Onne da ke jihar Ribas a kudu maso kudancin Nijeriya.


Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Onne,wanda aka shirya domin bayyana kayayyakin da aka kama tare da mika su ga hukumar da ta dace.


Yace bisa bayanan sirri da suka samu, kwantena mai lamba 165396 wadda ta zo daga kasar Turkiyya an samu bayanan akwai gurbatattun abubuwa a ciki da aka shigo dasu

Kwantenar da ke dauke da bindigun da alburusai da aka boye a cikin abubuwa daban-daban kamar su ’yar tsana, kayan daki da kayan aikin famfo an kama ta ne a tashar tashar Onne ranar 21 ga Yuni, 2024 wanda kudin su yakai kusan sama da biliyan hudu.


A dangane da wannan,akwai mutum uku da ake tuhuma suna hannu da zarar an kammala bincike za a kaisu kotun da ta dace domin gurfanar dasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp