Za a shafe shekaru 17 ba a yi aikin hajji cikin zafin rana ba bayan na shekarar 2025 - Hukumomin Saudiyya


Cibiyar kula da yanayi ta Saudiyya ta yi hasashen cewa aikin hajjin badi na 2025 ne zai zamo na karshe da za a gudanar cikin tsananin zafin rana.

Cibiyar ta ce za a gudanar da aikin hajjin 2026 cikin kwanakin sanyi da za a kwashe shekaru 8 jere ana aikin hajji ba tare da zafin rana ba, kamar yadda aka yi wadannan 8 ana kwala rana.

Kakakin cibiyar da ke kula da sararin samaniyar ta Saudiyya Hussein Alqahtani ya ce aikin hajjin zai shiga wani sabon aji na sauyin yanayi, wanda wataqila a iya kwashe kusan shekaru 17 kafin zafin rana ya dawo a yayin gudanar da aikin hajji.

Hakan na nufin za a gudanar da aikin hajjin badi 2025 cikin zafin rana, amma na badi waccan 2026 zai kasance lokacin ya sauya.

Post a Comment

Previous Post Next Post