Hukumar NDLEA ta kama mata masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a Katsina


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce a halin da ake ciki ana samu karin mata masu tu'ammali da miyagun kwayoyi a baya-bayan nan, inda ta ce har ma ta fara kamo wasu daga cikinsu domin a yi wa tufkar hanci cikin lokaci.

Shugaban hukumar na jihar Katsina Hassan Sani Abubakar ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai domin bikin makon yaki da tu'ammali da miyagun kwayoyi da majalisar dinkin duniya ta ware.

Shugaban hukumar ta NDLEA na jihar Katsina Hassan Sani Abubakar ya ce duk a cikin kokarin da suke yi na yaki da sha da fataucin kwayoyi, sun yi nasarar fasa taron wasu matasa da suke kokarin shigo da wata sabuwar hanyar shaye-shaye a fadin jihar Katsina.


Ya ce suna samun kalubale musamman daga 'yan cikin Unguwa idan ma'aikatansu suka je aiki a lungu sa sako na jihar a kokarin da suke yi ma kawar da dabi'ar shaye-shaye a cikin al'umma.

Shugaban hukumar ya ce sun yi nasarar kama mutane 1,344, da ake zargi da sha da kuma masu sayarwa wadanda daga cikin wannan jimilla akwai mata da abin ke nema ya ta'azzara.

Sauran kayan shaye-shaye, kamar kamar yadda Hassan Sani Abubakar ya bayyana akwai tabar wiwi, maganin tari na 'Codeine' da aka sauya wa samfuri daga na ruwa zuwa na 'kwaya' wato 'tablet'.

Shugaban hukumar ya kuma kara da cewa akwai mutane kimanin 106 da hukumar ta kai kotu da kuma wasu da yanzu haka an ma rigaya da an yanke musu hukunci suna can suna girbar abin da suka shuka.

Post a Comment

Previous Post Next Post