Buhun masara ya cike N100,000 a wasu kasuwannin Nijeriya


Masara tayi tashin gwouron zabi a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a makon nan ana sayar da buhu mai cin tiya 40 kan kudi ₦100,000 daidai, yayin da a makon jiya aka sai da ₦87,000, a mako guda an samu karin ₦13,000 a jihar da ke kudancin Najeriya.

Ita ma dai kasuwar Mai'adua jihar Katsina buhun masarar ya kusa cika ₦100,000, inda aka sayar da buhunta kan kudi ₦95,000 a satin nan da ke mana ban kwana, bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦84,000, karin ₦11,000 kenan aka samu.

To a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ₦85,000 aka sayi buhun masarar a makon nan, inda a makon da ya gabata aka saya ₦82,000, ita ma dai karin dubu 3 kenan aka samu a satin nan.

A kasuwannin jihohin Adamawa da Kaduna an sai da Buhunta ₦87,000 a wannan makon, amma farashin na makon jiya ya sha banban a kasuwannin, inda aka sayi buhun masara ₦85,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna a satin da ya shude, sai kuma kasuwar Karamar Hukumar Gombi a jihar Adamawa da aka saya ₦79-80,000.

Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka saya ₦145,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦150,000 aka sayi buhunta, an samu ragin ₦5000 kan farashin makon da ya wuce.

Su kuwa Jihohin Adamawa da Kano da jihar Kaduna da ma Lagos, kuɗin buhun Shinkafa 'yar gida ₦150,000 cif ne wannan makon, hakan kuwa batun yake a makon da ya shude.

Ita kuwa Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ke arewacin kasar da ake saidawa ₦86,000,bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦80,000

Sai dai farashin Shinkafar wajen bai sauya tufafi ba da na makon jiya wanda aka saya ₦85,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano.

An sayi buhun Shinkafar waje ₦78-80,000 daidai a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a satin nan da ke dab da ƙarewa, inda a makon jiya aka sai da kan kuɗi ₦75,000.

A Mai'adua jihar Katsina ₦81,000 ne kuɗin buhun Shinkafar waje a satin nan, bayan a satin da ya gabata aka sayar ₦78,000.

Bari mu kammala Farashin Shinkafar waje da kasuwar Mile 12 International Market Lagos, da aka saya ₦83,000.

Kwalin taliyar Spaghetti ma dai ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Lagos da aka saya ₦17,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka sai da ₦16,000 karin ₦2000 a mako guda.

Sai kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka saya ₦15,000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka saya ₦15,500
An samu ragin ₦500 kenan a makon nan.

A kasuwar Dawanau jihar Kano ₦13,500 ake sayar da kwalin taliyar a wannan makon,haka farashin yake a makon jiya.

Sai kasuwar Zamani da ke nan jihar Adamawa da aka sayi kwalin ₦14,000,inda a makon jiya aka saya ₦13,000 daidai.

To a kasuwar Giwa jihar Kaduna ma dai farashin bai sauya dana makon daya gabata da ake saidawa ₦14,000 cif.

Ga ma'abota cin kosai da alala kuwa Farashin farin wake ₦2200,000 ne a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a wannan satin,amma satin daya gabata ₦200,000 daidai a kasuwar.

Sai dai a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna kuwa ₦175,000 aka sayar da buhunta a makon nan,yayinda a makon jiya aka sai da buhun kan kuɗi ₦170,000 cif.

₦160-170,000 ake sayar da buhun farin wake a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a sati na, yayin da a satin da ya kare aka saya ₦160,000 daidai.

Da muka leka kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma mun taras cewa ana sayar da buhun waken N170,000 a satin Nan, yayin da makon da ya gabata aka saya N165,000.

DCL Hausa A'isha Usman Gebi

Post a Comment

Previous Post Next Post