'Yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zarginsu da kai wa yan bindiga makamai da alburusai a jihar Katsina

‘Yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zarginsu da kai wa yan bindiga makamai da alburusai a dazukan jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna kaiwa ‘yan bindiga makami makamai da alburusai a dajin Katsina.


Wadanda ake zargin su ne sun hada da Haladu Isah na kauyen Tsaskiya, karamar hukumar Safana, Abubakar Ahmed  Sha’iskawa, Barhim, Katsina; da Adamu Musa Ba’ude a Jamhuriyar Nijar.

a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq, kamen ya biyo bayan bayanan da aka samu a ranar 6 ga Afrilu, 2024, a ofishin 'yan sanda da ke Kaita kan munanan ayyukan mutanen uku.

A wata sanarwa da ya fitar ya ce cikin gaggawar ‘yan sanda sun kai dauki tare da samun nasarar gano wadanda ake zargin tare da cafke su a hanyar Dankama a karamar hukumar Kaita.


an gano wadan da ake zargin a hannunsu da kudi naira miliyan daya da dubu dari biyu da uku (N1,203,000.00k) da ake zargin na alburusai ne

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp