Kungiyar kananan hukumomi tace ba za ta iya biyan dubu N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba

Kungiyar kananan hukumomi tace ba za ta iya biyan dubu N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Kungiyar Kananan hukumomin Nijeriya (ALGON) ta ce kananan hukumomin kasar ba za su iya biyan mafi karancin albashin da kungiyar kwadagon ke nema ba.


Shugaban kungiyar na kasa, Aminu Muazu-Maifata, ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels Television.

Ya ce da kason da ake samu daga asusun gwamnatin tarayya, babu wata karamar hukuma da za ta iya biyan ma’aikata mafi karancin albashi na ₦62,000 da gwamnatin tarayya ke yi balle ma kungiyar kwadagon ta bukaci ₦250,000.


Muazu-Maifata ya ce wasu kananan hukumomin ba su fara biyan ma’aikatan su dubu ₦30,000 da aka amince a matsayin mafi karancin albashi tun a shekarar 2019 ba, kananan hukumomi da dama har yanzu ana biyan ma’aikata ₦18,000 a mafi karancin albashin.


Haka zaka sanya mafi karancin albashi mai yawa haka ba wani abu bane da zai dore domin da dama zai yi musu wahalar biya .

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp